Zulum ya naɗa kwamitin da zau raba tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa

Daga Sodiqat A’isha Umar
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya samar da kwamiti na musamman wanda zai dauki ɗawainiyar rabon kayan tallafi ga mutanen da iftila’in ambliya ya shafa a Maiduguri.
Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Bukar Tijjani ya fitar, gwamna Zulum ya bayyana cewe kwamitin mai mamboi 35 zai kunshi wakilai daga hukumomi da dama da suka haɗa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ICPC da DSS.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa masu ba shi shawara da wakilan hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC), ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa da ma’aikatar kudi da ta mata da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da sauransu.
Gwamna Zulum ya buƙaci mambobin kwamitin da su jajirce wajen sauke nauyin da aka ba su da kuma yin gaskiya.
Ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da ganin an sake gyara wurare kamar asibitoci da hanyoyi da kuma gadoji.
Mutane da dama dai, musamman masu hannu da shuni suka bayar da tallafin kuɗaɗe da kuma kayan abinci zuwa ga waɗanda ambaliyar Maiduguri ta shafa.