Zo ka ga misalin yadda ake yaƙi da media
Daga Misbahu El-Hamza
Ƴan Hamas sun saki wata Bayahudiya da suka kama mai shekaru 80 da ɗoriya. Da ta zo tafiya, sai ta juyo ta miƙawa wani ɗan Hamas hannu suka gaisa, sannan ta ce musu “shalom”. Wato aminci ya tabbata a gareku.
Bayan zuwanta Isra’ila, ƴan jaridu sun yi hira da matar wacce ta yi magana da yarensu na Yahudu, ƴarta kuma na fassara wa. Ta faɗi irin halin da ta tsinci kanta a zirin Gaza, da yadda ƴan Hamas suka mu’amalance ta.
#BBC da suka tashi wallafa kanun labaran, sai suka ce matar ta ce ta “fuskanci bala’i a hannun Hamas.”
#TRTWorld kuma sai suka ce matar ta ce ƴan Hamas “sun ce sun yi imani da al-Qur’ani, saboda haka ba za su cutar da su (Yahudawan da suka yi garkuwa da su) ba.”
#Channel4 suma yadda BBC ta ruwaito cewa an gallaza musu azaba, haka suka ruwaito nasu kanun labaran.
#SkyNews kuma ta wallafa bidiyo inda matar ke ba da labarin irin mutumta su da dakarun Hamas suka yi. Ta ce an girmama su, an kula da lafiyar su, da sauransu.
Abin Lura:
Da BBC da Channel 4 manyan jaridu ne masu shalkwata a Birtaniya kuma ƙarƙashin gwamnatin Birtaniya suke. Saɓanin Sky News wacce itama shalkwatanta na Birtaniyar amma ta ƴan kasuwa ce (ƴan Amurka). TRT World kuma ƙarƙashin gwamnatin Turkiyya ta ke.
Abin da wannan ke nufi shi ne, dukkanin muradun gwamnatin Birtaniya dole ne BBC da Chennel 4 su ba da nasu gudunmawar wajan tabbatar da su. Haka ma TRT World ga gwamnatin Erdogan na Turkiyya. Sky News kuma ba tilas bane su bi muradun gwamnatin Yamma — amma suna bi.
Gwamnatin Birtaniya na goyon bayan luguden wutar da gwamnatin Isra’ila ke yi kan Falasɗinu. Saboda haka, BBC da Channel 4 dole su ƙarfafa wannan muradin na gwamnatin Firaminista Rishi Sunak. Ita kuma, TRT muradun Erdogan take karewa na goyon bayan Falasɗinawa.
To tunda aka fara gwabza wannan yaƙin, haka gidajen jaridu ke ta fafatawa. Kan gaba wajan nuna halin da Falasɗinawa ke ciki sune misalin Al Jazeera da TRT. Su kuma BBC da CNN ta Amurka sun fi mai da hankali kan nuna halin da Isra’ila ke ciki.
Ko batun bam da aka sauke kan asibitin Al Ahli na cikin Gaza, kowanne cikin manyan jaridunnan sai da ya fitar da nashi binciken, kuma ya tsaya tsayin daka cewa hakan ne daidai; waɗannan na nuna laifin Hamas ne, waɗancan na nuna laifin Isra’ila ne.
Idan haka abin ya ke, shin yaya kuke kallon rawan da media ke takawa a al’amurra daban daban na rayuwar mu?🤔
продамус промокод скидка продамус промокод скидка .
Платежный модуль геткурс промокод http://www.platezhnyj-modul-getkurs-promokod.ru .
продамус промокод скидка promokod-prod.ru .