Zargin cin hanci: Tinubu ya gayyaci ministan cikin gida
Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya gayyaci ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo zuwa fadar shugaban kasa.
Wannan sammacin ya biyo bayan cece-kucen da ya dabaibaye ma’aikatar jin kai, wadda rahotanni suka ce ta bayar da kwangilar da ta kai naira miliyan 438, New New Planet Projects Ltd, kamfanin da aka ce ministan cikin gidan yana da hannu a ciki.
To sai dai har zuwa wannan lokaci ba mu tabbatar da ainihin dalilin da ya sa shugaban kasar ya gayyaci ministan ba.
Amma dai TCR Hausa ta ga rubuce-rubuce da wasu ƴan Najeriya suka yi a shafin X da ke nuna suna so shi ma a bincike shi game da wannan baɗakalar.
Daga cikin masu irin waɗannan kiraye-kirayen akwai Audu Bulama Bukarti inda ya ce, “Dole ne a dakatar da Ministan Harkokin Cikin Gida ma. A lokacin da aka yi hira da shi a gidan Talabijin na Channels, ya bayyana har abin da bai yi niyya ba, inda ya fito da gaskiya. Ya gaskata cewa shi ne ya mallaki New Planet Project Ltd kuma ya amince da matsayin matarsa a matsayin darakta.”