January 24, 2025

Zargin cin hanci: Tinubu ya dakatar da shugabar hukumar zuba jari Halima Shehu

2
images-2024-01-02T122147.493.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaba Bola Tinubu ya amince da dakatar da Halima Shehu a matsayin babbar jami’a (Shugaba) da kuma kodineta na Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA).

Tinubu ya amince da dakatarwa tare da fara binciken Malama Shehu nan take, yayin da Dr Akindele Egbuwalo manajan shirin N-Power na kasa aka nada shi a matsayin shugaba har sai an kammala bincike, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Shugaba Tinubu ne ya nada Halima Shehu a watan Oktoba 2023, kuma Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin nata a ranar 18 ga Oktoba, 2023.

Halima ta yi aiki a matsayin mai kula da shirin Canjin kudi na kasa (Conditional Cash Transfer Programme), inda ta yi amfani da kwarewarta ta fannin banki da aikinta wajen ganin an daidaita tsarin.

2 thoughts on “Zargin cin hanci: Tinubu ya dakatar da shugabar hukumar zuba jari Halima Shehu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *