Zargin cin hanci da rashawa: An hana ministar da aka dakatar ganin Tinubu
Daga Sabiu Abdullahi
Rahotanni da ke fitowa daga Abuja na nuna cewa an hana Betta Edu, ministar harkokin jin kai da yaki da fatara da aka dakatar a ranar Litinin, ganawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Hakan ma zuwa ne jim kadan bayan da kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya sanar da dakatar da ita.
A cewar gidan talabijin na TVC, yunkurin Edu na ganawa da shugaban kasar bai yi nasara ba, kamar yadda aka dauka a wani faifan bidiyo da ke nuna yadda ta taso daga fadar gwamnatin cikin bakar mota bayan hana ta shiga.
Takaddamar dai ta kunno kai bayan Edu ta shiga komar doka sakamakon bullar wata takarda da Ministar ta sanya wa hannu, inda ta ba da umarnin cire kudi N585,189,500.00 zuwa wani asusun sirri na Bridget Mojisola Oniyelu.
Takardar da aka fallasa ta haifar da tambayoyi game da hada-hadar kudi a karkashin ma’aikatar kula da jin kai da yaki da fatara ta tarayya.