Zanga-zangar nuna adawa dadokar ƙarin haraji a Kenya
Daga Mustapha Mukhtar
A yau Talata ne dubban samari a babban birnin ƙasar Kenya suka gabatar da zanga-zangar ƙin jinin dokar sabunta haraji ta ƙasar da ake ƙoƙarin sakawa hannu a ƙarshen makon nan da ake ciki.
Zanga-zangar wacce ta yi sanadiyyar ƙona wani ɓangare na ginin majalisar Ƙasar, da wani ɓangare na ofishin gwamnan Nairobi.
An ga gawarwakin mutum huɗu, masu rahoto na cewa wanda suka mutu na iya zarta wannan adadi.
Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Samuel Ruto ke wajen birnin Nairobi.