January 15, 2025

Zanga-zanga ta sake ɓarkewa a Ribas don nuna adawa da zaɓukan ƙananan hukumomi da ke gudana

97
IMG-20241005-WA0028

Daga Abdullahi I. Adam

A jiya Juma’a ne aka gudanar da wata zanga-zanga ta nuna goyon bayan zaɓen ƙananan hukumomi da ke gudana yanzu haka a jihar Ribas.

Hakan ya zamela kamar wani martani ne ga wata ƙungiya da ta yi zanga-zanga a ranar Asabar ɗin da ta gabata don nuna rashin amincewa da tsarin zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Ribas ke gudanarwa.

Zanga-zangar ta jiya Juma’a ta gudana ne a kan titunan garin Fatakwal, yayin da masu zanga-zangar suka mamaye ofishin hukumar zaɓe na jihar, RSIEC, domin nuna goyon bayansu ga zaɓen.

Sai dai ana cikin gudanar da zaɓen na yau Asabar sai ga wata sabuwar zanga-zangar wacce galibi matasa ne suka shirya ta, waɗanda suka taru a unguwar Polo Club da ke GRA a Fatakwal kafin su nufi tsakiyar unguwar inda suke bayyana cewa zaɓen da ke gudana ba halastacce ba ne.

Masu zanga-zangar sun dage cewa ba a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar ba, inda suka jaddada cewa sun dogara ne da hukuncin da babbar kotun tarayya ta Abuja ta yanke, wanda ya umarci ‘yansanda da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar da kada su shiga zaɓen.

Da yake magana kan lamarin, ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, mai suna Bobmanuel, ya ce, “Mu ‘yan ƙasa ne masu bin doka; shi ya sa ba ma shiga zaɓen. Mun taru a nan ne domin mu shaida wa duniya cewa ba a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Ribas ba.”

Rahotanni daga jihar ta Ribas suna nuni da cewa tuni dai aka kammala zaɓen na yau a sassa da dama na jihar inda a yanzu haka ake dakon hukumar zaɓe ta jihar domin tattara tare da sanar da sakamakon zaɓen.

97 thoughts on “Zanga-zanga ta sake ɓarkewa a Ribas don nuna adawa da zaɓukan ƙananan hukumomi da ke gudana

  1. продамус промокод скидка на подключение [url=https://severussnape.borda.ru/?1-4-0-00000385-000-0-0-1734553080/]https://vip.rolevaya.info/viewtopic.php?id=7107#p1[/url] .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *