Zanga-zanga: Shugaba Tinubu ya gana da malaman addini

Daga Abdullahi I. Adam
Malamai daga ƙungiyoyin addinin Musulunci sun sami ganawa da shugaba Tinubu a fadarsa da yammacin Alhamis ɗin nan.
A yayin ganawar, shugaban ƙasa Tinubun ya bayyana cewa marasa kishin ƙasa ne ke neman a gudanar da zanga-zangar domin su mutane ne da suka fifita buƙatunsu a kan na ƙasa.
Shaikh Abdullahi Bala Lau, wanda shi ne jagoran malaman a yayin tafiyar ya sanar da cewa za su dage da saka Najeriya cikin addu’o’i domin ganin ta fita daga halin da ta ke ciki.