November 8, 2025

Zamfara: Gobara Ta Tashi a Kasuwar Talata Mafara

MixCollage-11-Jan-2025-04-45-PM-2105.jpg

Daga Sashen Hausa na Citizen Reports

Wata gobara da ta tashi a kasuwar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara da yammacin ranar Talata ta jikkata fiye da mutum 25 da suka samu munanan ƙonewa, yayin da da dama daga cikinsu ke karɓar magani a Asibitin Karamar Hukumar Talata Mafara.

Masanin tsaro, Zagazola Makama, wanda ya wallafa rahoton a shafinsa na X a ranar Laraba, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana bayan wani harbi da abin fashewa da suka firgita jama’a.

“Mun ji wani ƙarar fashewa mai ƙarfi, sai gobara ta bazu cikin kasuwa cikin ƙanƙanen lokaci. Mutane suka rika gudu a kowane ɓangare, amma da dama sun makale cikin wutar,” in ji wani ɗan kasuwa da ya shaida lamarin.

Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta tabbatar da afkuwar gobarar, inda ta bayyana cewa fiye da mutum 25 sun samu ƙuna kuma an gaggauta kai su asibiti don kula da lafiyarsu.

3 thoughts on “Zamfara: Gobara Ta Tashi a Kasuwar Talata Mafara

  1. I’ve been following your blog for quite some time now, and I’m continually impressed by the quality of your content. Your ability to blend information with entertainment is truly commendable..

Comments are closed.