December 7, 2025

‘Za mu sake duba lamarin ƙarin kuɗin wutar lantarki’

IMG-20240509-WA0021.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Gwamnatin tarayya ta ce za ta sake duba maganar ƙarin kuɗin lantarki da aka yi wa ‘yan rukunin Band A a watan da ya gabata sakamakon zanga-zangar da ‘yan ƙungiyar ƙwadago suka gudanar a jiya Litinin.

Babban sakatare a ma’aikatar lantarki Mamudah Mamman da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi a Abuja, bayyani ya shaida cewa, tuni majalisar ƙasa ta nemi gwamnati ta ƙara neman shawarar masu ruwa da tsaki kan ƙarin.

A safiyar litinin ne mambobin ƙungiyar ta NLC suka yi wa ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki tsinke a faɗin ƙasar, ciki har da na Abuja.

A watan Afrilu ne hukumar Narc ta amince da ƙarin N225 kan kowane kwh ɗaya daga N66, kafin daga baya a rage shi zuwa N206.80.

58 thoughts on “‘Za mu sake duba lamarin ƙarin kuɗin wutar lantarki’

Comments are closed.