‘Za mu inganta ƙarfin intanet a ƙasashen Afirka’
Daga Sodiqat Aisha Umar
Gwamnatin Amurka ta bayyana shirinta na inganta karfin Intanet a kasashen Afirka zuwa kashi 80 ciki 100 nan da shekarar 2030.
Wannan dai ya zo ne cikin wata sanarwar da Mataimakiyar Shugabar Amurka, Kamala Harris, ta fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar na zuwa ne bayan shekara guda da ziyarar da ta kai nahiyar Afirka, a dai_dai lokacin da suka zanta da Shugaban Kenya, William Ruto a birnin Washington.