Za mu gurfanar da Emefiele kan sabunta takardun naira—EFCC

Daga Sodiqat Aisha Umar
Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa arzikin kasa ta’annati, EFCC, za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele ranar Laraba nan, bisa bayar da izinin buga sabbin takardun naira na miliyan 684.5 a kan naira biliyan 18.96.
Tun da farko, an tsara gurfanar da shi ne ranar 30 ga watan Afrilu da ya gabata amma aka ɗage ranar, bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kotun da kuma ɓangarorin.
A tuhume-tuhumen huɗu da aka shigar a kansa, EFCC ta yi zargin Emefiele ya yi burus da umarnin kotu da nufin jefa jama’a cikin mawuyacin hali lokacin aiwatar da tsarin sauya takardun naira da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi.
EFCC ta kuma zargi Emefiele da ba da izinin cirar naira biliyan 124.9 daga asusun bai ɗaya na ajiyar kuɗaɗen shiga na gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
An kuma zarge shi da yin amfani da matsayinsa wajen amincewa da kwangilar siyan motoci 43 a kan kuɗi naira biliyan 1.2 daga 2018 zuwa 2020.
Truly appreciate your well-written posts. I have certainly picked up valuable insights from your page. Here is mine YW9 about Thai-Massage. Feel free to visit soon.