June 14, 2025

Za ku yi nadamar barin NNPP – Kwankwaso ga Kawu Sumaila da sauran ‘yan majalisa

MixCollage-14-Feb-2025-10-09-AM-3360.jpg

Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ‘yan majalisar tarayya da suka bar jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki za su yi nadamar wannan matakin da suka dauka.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin da yake karbar bakuncin daruruwan magoya bayan jam’iyyar NNPP daga karamar hukumar Takai a jihar Kano, wadanda suka ki bin Sanata Kawu Sumaila zuwa jam’iyyar APC.

Cikin wadanda suka sauya sheka daga NNPP zuwa APC akwai Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, da Alhassan Rurum da wasu ‘yan majalisa.Kwankwaso ya bayyana sauya shekar a matsayin babbar cin amana da ake aikatawa a siyasa, inda ya ce: “Kano ta Kudu ta zama darasi. Masu kada kuri’a sun ki karbar Taliya, Naira dari biyu da Atamfa, suka yi hakuri suka zabi NNPP.”

Ya ci gaba da cewa: “Amma wasu daga cikinmu da suka ci zabe sun zabi su bar talakawa, su koma wurin masu neman amfanar kansu da iyalansu kawai.”

“Babu zunubi mafi muni a siyasa kamar ka bar jam’iyyar da ta ba ka dama da goyon baya, ka koma wa wata jam’iyya saboda kawai son zuciya. Wannan shi ne mafi girman cin amana,” in ji Kwankwaso.