January 14, 2025

Za a tsaurara matakan tsaro a iyakokin Najeriya saboda zanga-zanga a wani mataki na gudun shigowar  bata-gari

0
images-6-5.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumomin Nijeriya sun ba da umarni a tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin ƙasar da maƙotanta a yayin da wasu al’ummar kasar ke shirin gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ta addabe su.
 
Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, KT Udo, ya fitar ta ce shugaban hukumar yana mai bayar da umarnin ƙara tsaro a cikin ƙasar da ma kan iyakokinta da ƙasashe masu makwabtaka da Najeriya.
 
A cewarsa, “Babban Kwanturola na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, KN Nandap, ya bayar da umarni ga dukkan shugabannin yankuna da na jihohi da na gundumomi a faɗin ƙasar nan su ƙara sanya ido sannan su sanya ƙarin matakan tsaro sakamakon shirin da wasu ƙungiyoyi suke yi na gudanar da zanga-zanga a Nijeriya.”
 
Ya ƙara da cewa “Babban Kwanturola ya kuma bayar da umarni ga manyan Kwanturololi da ke kan iyaka su tabbatar cewa jami’an da ke aiki a kan iyakoki sun tashi tsaye wajen hana duk wasu ɓata-gari daga ƙasashen waje shigowa ƙasar nan domin aiwatar da mugun nufinsu.”
 
Sanarwar ta yi umurni ga jami’an hukumar da su yi aiki da basira da nuna ƙwarewa kuma kada su ci zarafin kowa.
 
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta ɗauki wannan mataki ne bayan sauran jami’an tsaron ƙasar ciki har da rundunar ‘yan sanda da rundunar soji sun ja kunnen masu shirin gudanar da zanga-zangar, suna masu zargin cewa akwai yiwuwar ta rikiɗe zuwa tarzoma kamar yadda ya faru a Kenya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *