Za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Filato a watan Oktoba
Daga Abdullahi I. Adam
Hukumar zaɓe ta jihar Filato, PLASIEC, ta tabbatar da kammala shirye-shirye don gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ƙananun hukumomi 17 da ke faɗin jihar.
Shugaban hukumar zaɓe ta jihar ne Plangji Cishak ya sheda ma manema labaru hakan a safiyar yau Laraba a wani taro na masu ruwa da tsaki da ke gudana a Jos.
Kamar yadda Plangjin ya faɗa, za’a gudanar da zaɓen ne a dukkanin ƙananan hukumomi 17 na jihar waɗanda a halin yanzu su ke ƙarƙashin jagorancin kantomomi na wucin gadi.
Shugaban hukumar zaɓen ya jaddada ma wakilan jam’iyyaun siyasar da ke halartan taron irin ayyukan da hukumar ta gabatar inda ya ƙara da cewa “A yau za mu gabatar maku da abu mafi muhimmanci da doka ta tanadar game da wannan zaɓe: wato tsara zaɓe. A yau mu ke sanar da ku cewa zaɓen bana zai gudana a watan Oktoba.”
“Kamar yadda Sashe na 64 na dokokin zaɓen jihar Filato ya tanada, haƙƙinmu ne, daidai da kashi na 4 na kundin, Sashe na 16, Sakin layi na 1 da 22, a ƙaramin sashe na 1 na dokokin hukumar zaɓe ta jiha (PLASIEC) na 2016 da kuma sashe na 197 (1da 2) na kundin tsarin mulki na ƙasa na 1999 kamar yadda aka sauya masa fuska a 2023 da kuma dokar zaɓe ta 2022, hukumar zaɓe ta jihar Filato na farin cikin sanar da shuwagabann jam’iyyaun siyasa da kuma al’umma gaba ɗaya cewa za’a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ɗaukacin ƙananan hukumomi 17 na jihar Filato a ranar Laraba 9 ga Oktoba 2024, daga ƙarfe 8:00 na safe har zuwa ƙarfe 3:00 na marece,” inji shugaban hukumar zaɓen.
Hukumar ta nemi masu sha’awan takara da su cike takardun nuna sha’awan takarar Wanda za su samu a shalkwatan hukumar da ke lamba 7, layin John Mark Sanchiro da ke Jos daga ranar Litini 5 ga watan Agusta 2024 daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 4:00 na marece a kullum.
Haka zalika, hukumar zaɓen jihar ta sanar da cikakken jadawalin yadda ake sa ran gabatar da dukkanin shirye-shiryen zaɓen na wannan shekara.
Daga ƙarshe shugaban hukumar zaɓen ya nemi dukkanin jam’iyyun siyasa da su ba ma hukumar goyon baya don gudanar da zaɓen lami lafiya.
Hi colleagues, fastidious article and good urging commented at this place, I am truly enjoying by these.
официальный сайт драгон мани казино
This is my first time pay a visit at here and i am in fact impressed to read everthing at single place.
онлайн казино Dragon Money
Hi, after reading this amazing post i am as well cheerful to share my know-how here with mates.
топ мэйкер накрутка пф
Fantastic blog you have here but I was wondering if you knew of any message boards that cover the same topics talked about here? I’d really love to be a part of group where I can get comments from other knowledgeable people that share the same interest. If you have any suggestions, please let me know. Many thanks!
большие сиськи
Useful information. Lucky me I found your website accidentally, and I am stunned why this twist of fate didn’t came about in advance! I bookmarked it.
накрутка пф москва
Simply desire to say your article is as surprising. The clarity to your put up is simply cool and i can assume you’re knowledgeable on this subject. Well with your permission let me to take hold of your feed to keep up to date with forthcoming post. Thanks a million and please continue the rewarding work.
смотреть кино онлайн