January 24, 2025

Za a fara shirya finafinan kurame a Kano

0
images-4-4.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta jihar Kano ta bayyana cewa tana nan tana himmar fara shirya fim ɗin kurame a jihar.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ne ya bayyana hakan lokacin da ƙungiyar kurame ta kai masa ziyara a ofishinsa.

A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar, El-mustapha “ya yi wa mambobin ƙungiyar alƙawarin haɗa su da dukkan wani da ake tunanin zai iya taimaka musu a ciki da wajen masana’antar Kannywood.”

Lokacin da a yake magana yayin ganawarsu, jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar Kurame Rabi’u Aliyu Adam ya ce suna da gudummawar da za su iya bai wa al’umma musamman masu buƙata ta musamman.

“Manufar fara shirya finafinan ita ce samar da aiki ga kurame baya ga ilimantarwa tare da nishaɗantar da sauran masu buƙata ta musamman,” in ji shi.

Rabi’u ya tabbatar wa El-Mustapha da cewa tuntuni suka fara shirya wasu finafinai na kurame ta hanyar amfani da wayar salula, kamar yadda sanarwar ta bayyana, kuma ya nemi taimakon gwamnatin Kano wajen cikar burinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *