January 15, 2025

Za a fara jigilar maniyyatan aikin Hajji —NAHCON

6
IMG-20240503-WA0019.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa, NAHCON, ta bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa don fara jigilar maniyyata daga Najeriya don soma aikin hajjin bana kamar yadda aka tsara.

Shugaban hukumar, Alh. Jalal Ahmad Arabi, ne ya bayyana haka jiya a Abuja yayin wani taron bita kan aikin hajjin wanda aka saba gudanarwa duk shekara.

Kamar yadda shugaban hukumar ya faɗa “bana maniyyata 65,000 ne za su sauke farali daga Nigeria”, kuma ana sa ran za su fara isa birnin Madina ne inda za su shafe kimanin kwanaki huɗu domin ziyara.

Haka nan kuma, shugaban ya ce jigilar maniyyatan za a yi ta ne a tashoshin jirage goma a faɗin ƙasar, kuma ana sa ran fara jigilar ne ranar 15 ga watan nan na Mayu da muke ciki.

6 thoughts on “Za a fara jigilar maniyyatan aikin Hajji —NAHCON

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *