January 14, 2025

Za a fara cire wa masu tura kuɗi ta banki harajin tsaron intanet a Najeriya

11
image_editor_output_image1530788143-1715178582065.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Babban Bankin Najeriya CBN ya bai wa bankuna a fadin ƙasar umarni da su fara cire kashi 0.5 cikin 100 a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki a matsayin kuɗaɗen tabbatar da tsaro ta intanet.

Cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun Chibuzor Efobi, Daraktan kula da tsarin biyan kuɗi da Haruna Mustafa, Daraktan kula da manufofin kuɗi, babban bankin ya ce za a fara aiwatar da wannan tsari ne nan da makonni biyu masu zuwa.

A cewar CBN, kuɗin da za a cira domin tara harajin tsaron intanet ya zo ne sakamakon amincewa da dokar yaƙi da laifukan intanet ta 2024 da aka yi wa gyaran fuska.

Sanarwar ta ce za a zuba kuɗin da aka cira ne a asusun tsaron intanet na ƙasa wanda zai kasance a ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Tsarin bai shafi masu karɓa da biyan bashi ba da kuɗaɗen albashi da kuma mutumin da zai tura kuɗi daga asusun ajiyarsa na banki zuwa wani asusun nasa na daban da kuma masu tura kuɗi zuwa wani asusun na banki ɗaya.

11 thoughts on “Za a fara cire wa masu tura kuɗi ta banki harajin tsaron intanet a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *