December 7, 2025

Za a ƙara farashin barasa a Najeriya

IMG_8528.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Kamfanin ‘Nigerian Breweries Plc’ ya fitar da sabon sanarwar sake duba farashi ga duk kwastomomin sa na shiyyar Yamma.

A cikin wata wasika mai kwanan watan Litinin, Fabrairu 12, 2024, bitar farashin, wanda zai fara aiki daga Litinin, Fabrairu 19, 2024, ana ganin ya zama dole ne don daidaita tasirin karuwar kudaden samar da basasar.

“Wannan na zuwa ne don sanar da ku cewa an tilasta mana mu sake duba farashin wasu kayayyakinmu daga ranar Litinin, 19 ga Fabrairu, 2024.

“Wannan bita ta zama dole saboda ci gaba da hauhawar farashin da ake samu da kuma buƙatar rage tasirin lamarin,” kamar yadda aka ambati daga sanarwar.

Sai dai kuma kamfanin ya tabbatar wa abokan cinikayyarsa cewa waɗanda suka biya cikakken oda kafin ranar da aka ƙayyade za a ba su kayan s tsohon farashi.