#ZaɓenAmurkaNa2024: Tinubu Ya Taya Trump Murna Kan Sake Lashe Zaben Shugabancin Amurka
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya taya Donald Trump murnar sake lashe zaben shugabancin kasar Amurka, inda ya zama Shugaban kasa na 47.
Tinubu ya bayyana fata cewa wa’adin Trump na biyu zai kara dankon alaka tsakanin Najeriya da Amurka yayin da kasashen biyu ke fuskantar kalubale da damammaki na duniya.
Da yake tsokaci kan nasarar Trump a zaben, Tinubu ya ce wannan “na nuna amana da kwarin gwiwa da mutanen Amurka suka nuna a kan jagorancinsa.”
Ya yaba wa ’yan Amurka kan jajircewarsu wajen kare kimar dimokuradiyya.
Shugaban Najeriya ya bayyana fatan cewa dawowar Trump a Fadar White House zai kawo “dangantakar tattalin arziki mai inganci da taimakon juna tsakanin Afirka da Amurka,” yana mai jaddada kwarewar Trump a matsayin tsohon shugaban kasa na 45.
Yayin da yake yabawa da irin tasirin Amurka wajen tsara al’amuran duniya, Tinubu ya ce yana da yakinin cewa Shugaba Trump zai karfafa “zaman lafiya da arziki” a duniya baki daya.
Wannan sakon taya murnar na nuna fatan Najeriya na samun karuwar hadin kai da ingantacciyar alaka da Amurka karkashin sabon shugabancin Trump.