Yunwa na barazanar kashe Falasdinawa 800,000 a Gaza
Daga Sabiu Abdullahi
Mazauna birnin Gaza da kewaye 800,000 na fuskantar barazanar mutuwa saboda shiryayyar manufar Isra’ila na horar da su da yunwa da kishirwa, kamar yadda wani rahoton TRT Hausa ya rawaito a yau Lahadi.
Wata sanarwa da ofishin watsa labarai naaya fitar, ya bayyana cewa Gaza da arewacinta na bukatar motocin abinci 1,300 a kullum domin magance matsalar yunwa.
Ta bayyana cewa arewacin Gaza kadai na bukatar manyan motoci 600 na abinci sai kuma birnin na Gaza motoci 700.
Idan ba a manta na dai, Isra’ila ta shafe tsawon kwanaki 100 tana ci gaba da kai munanan hare-hare ba kakkautawa a Gaza
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 23,843 da raunata mutum 60,317.