Yau jirgin Tinubu zai tashi zuwa Chadi don rantsar da sabon shugaban ƙasa
Daga Sodiqat Aisha Umar
Shugaban Bola Tinubu zai yi tafiya zuwa ƙasar Chadi a yau Alhamis nufin shaida bikin rantsar da Mahamat Déby a matsayin shugaban ƙasar.
Idan ba a manta ba, farkon wannan watan nan na Mayu ne aka ayyana Mahamat a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 6 ga wata Mayu.
Wannan ne karo na farko da Tinubu zai tafi Chadi tun bayan zama shugaban ƙasa a watan Mayun 2023.