Yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƙungiyoyin ƴanbindiga 4 a Zamfara tana samun cikas
Abdulrazak Namadi Liman
Rahotanni sun ruwaito cewa mummunar hamayyar da ke tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan bindiga da ke ta’addanci a jihar Zamfara ya kara kamari inda wasu kungiyoyi hudu da suka firgita suka yi gargadin musgunawa juna.
Wasu majiyoyin leken asiri sun shaida wa kafar Zagazola Makama cewa, wasu daga cikin kungiyoyin kuma sun yi watsi da yiwuwar kulla yarjejeniyar zaman lafiya a kan sauran, yayin da suke sanar da ci gaba da fafatawa da sauran.
A ranar Asabar da ta gabata, 14 ga Afrilu, 2024, wakilan kungiyoyin uku daga cikin hudu – Dan Karami Gwaska da Alhaji Shingi – suka hallara a kauyen Usu da ke karamar hukumar Birnin-Magaji domin tattaunawa a tsakaninsu.
Kungiyar Bello Turji ba ta halarci taron ba. Ado Aleru ya wakilci kungiyar Alhaji Shingi; Bello Tagoje ya wakilci kungiyar Kachalla Halilu; yayin da Ardo Na-shawari, Alhaji Ali, Alhaji Shamago da d
Dan Karami Gwaska suka wakilci kungiyar Gwaska.
Kungiyar Shingi, wanda Ado Aleru ya wakilta, ta yi gargadi ga kungiyar Gwaska cewa kada ta sake takawa zuwa ga wata al’umma, in ban da Tsanu da Rukudawa na karamar hukumar Zurmi.
Sun kuma yi gargadin cewa idan Gwaska ya yi watsi da gargadin da suka yi, za su kashe shi da wasu daga cikin mutanensa.
Don ci gaba da fafatawa da shugabannin ‘yan bindiga uku, Ado Allero, Dan Yusufa da Mali sun riga sun ajiye mutanensu a Arewacin Tsafe, a shirye-shiryen tunkarar duk wata arangama.
A matsayin wani sharadi na zaman lafiya, kungiyar ta Shingi ta bukaci Dan Karami Gwaska ya mayar wa wani Hassan shanun da ya sace a Bafashi na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Sun kuma bukaci Dan Karami Gwaska ya mayar wa Sani Dangote makaman da ya kwashe a makon da ya gabata; sannan kuma ya sayi sabbin babura a matsayin diyya ga wadanda ya kona na mutanen Dangote.
Kungiyar Dan Karami Gwaska ta amince da dukkan sharuɗɗan.
Sai dai Bello Turji, wanda bai halarci taron ba, ballantana ya tura wakilai, ya yi watsi da yiwuwar samun zaman lafiya tsakaninsa da Gwaska, inda ya tabbatar da cewa zai ci gaba da farautar Gwaska domin ya kashe shi.