January 14, 2025

Yarinyar da aka zaƙulo daga ɓuraguzan gini a Gaza tana samun kulawa

0
18289717_0-0-760-428.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Yarinya Bafalasɗiniya Hala Hazem Hamada, ‘yar shekara 15, da aka zaƙulo daga ɓaraguzan gine-gine a Gaza kwanaki kaɗan bayan da Isra’ila ta kashe danginta tana samun dauƙi.

Yarinyar dai ta an ba da labarin yadda ta sha daga baraguzan gine-ginen da dakaru da motar katafila ta Isra’ila suka rugurguza.

A cewar TRT Afirka, Hala ta fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, sojoji sun yi amfani da lasifikar wajen kiran mazauna yankin da su tsere daga wajen.

To dai dai kafin ita da danginta su dauki matakin yin hakan, “gidan ya fara rushewa a kanmu”, inda motar katafilar Isra’ila ta fara ruguza gine-ginen.

“Dakarun sun kai wa kowa hari a gidan amma ban da ni da kanwata,” in ji ta. “Yar’uwata Basant ta ce da ni, “Na tsorata, ki cece ni, ba zan iya motsawa ba, baraguzan ginin nakan ƙafafu, kuma mahaifina yana kan ƙafata, ba zan iya motsawa ba.”

Har yanzu dai Isra’ila na ci gaba sa yin luguden wuta a yankin na Gaza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *