March 28, 2025

Yara biyu sun rasa rayukansu sakamakon rushewar masallaci a Legas

IMG-20240527-WA0005.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar


Yara mata biyu sun rasu yayin da wasu mutum biyar suka samu raunuka a jiya Lahadi sanadiyyar rushewar wani masallaci a unguwar Papa Ajao da ke birnin Legas.

Daya daga cikin manyan jami’an Hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas, Olatunde Akinsanya, ya bayyana wa manema labarai cewa daya daga cikin yaran da suka rasu ta rasa ranta ne nan take a inda lamarin ya faru yayin da dayar ta rasu a lokacin da aka isa da ita asibiti.

Masallacin mai hawa biyu ya rufta ne bayan wata motar rushe gine-gine da ke aikin fadada titi ta tokare shi bisa kuskure.