Yanayin tsaro ya sa Gwamnan Benue neman ƙarin jami’an tsaro a jihar
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamna Hyacinth Alia na Benue ya yi kira da a tura karin sojoji da karin sansanonin tsaro a wasu sassan jihar Benue domin magance matsalolin tsaro da suka addabi jihar.
Mista Alia ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga babban hafsan sojin kasar, COAS, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ranar Talata a Abuja.
Ya bukaci a kafa sansanonin gudanar da ayyukan tsaro a kananan hukumomin Guma, Logo, Ukum da Kwande don taimakawa wajen dakile matsalar tsaro a yankunan.
Ya ce mutanen Benue manoma ne sannan galibin yankunan da za a iya nomawa a Benue sun zama ba sa zaunuwa ga manoma saboda barazanar ‘yan fashi da tashin hankali daga makiyaya.
A cewarsa, ana kashe mutane biyu zuwa biyar ko fiye a kowane mako sakamakon tashin hankalin da wadannan kungiyoyi ke yi, wanda a wasu lokuta ‘yan jaridu ba sa bayyanawa.