‘Yan Shi’a sun kai koke ga EU, UN da NHRC kan cire wa mata Hijabi da cin zarafin da suke zargin ƴansanda sun musu

Daga Sabiu Abdullahi
Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a, ta kai ƙara wa kungiyar Tarayyar Turai, Majalisar Dinkin Duniya, da Hukumar Kare Hakkokin Bil’adama ta Kasa (NHRC) kan zargin cire hijabin mata Musulmi da karfi da kuma cin mutuncin Musulunci.
A cikin wata takardar ƙara mai dauke da kwanan watan Satumba 4, 2024, mai dauke da sa hannun Fatima Aliyu Adam a madadin kungiyar Academic Forum na kungiyar, kungiyar ta bukaci da a gudanar da bincike mai zurfi kan cire hijabin mata Musulmi da ƙarfi da ‘yan sandan FCT suka yi a ranar 26 ga Agusta, 2024, kamar yadda aka gani a bidiyo da hoto.
Koken dai ya zargi Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun da kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh, da laifin yiwa mambobinsu mata da aka kama a ranar 25 ga watan Agustan shekarar 2024 a taron Symbolic Arba’een na Abuja da cin fuska ta hanyar cire musu hijabi da ƙarfi.
Wasikar ta ce, “Muna rubutu ne domin mu kawo wa babban sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa, batun cire hijabi da ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja suka yi da karfi.
“Wannan hukunci da jami’an ‘yan sandan Najeriya suka yi na kama wasu ‘yan uwa mata Musulmi da gangan ba su da hijabi a rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, da kuma yaɗa hotuna da bidiyo daga wurin, ba wai kawai wadanda abin ya shafa ba, har ma addinin Musulunci gaba ɗaya.”
Kungiyar ta bukaci da a gudanar da binciken kwakwaf kan lamarin, inda ta bayyana cewa yana iya haifar da rikici da rigingimu a kasar.
Sun kuma bayyana cewa abin da manyan jami’an ‘yan sandan biyu suka aikata ya kai ga cin mutuncin addinin Musulunci a Najeriya.