‘Yan Sanda Sun Kama Matashi Bisa Zargin Kashe Jami’in Tsaron Sa-Kai a Kano

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta cafke wani matashi bisa zargin daba wa jami’in tsaron sa-kai wuƙa har lahira a filin Idi.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta bayyana cewa wanda ake zargi, mai shekaru 20, ya kai wa jami’in hari ne yayin da yake tsaron tawagar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, bayan sallar Idi a yau Lahadi.
Haka nan, wani jami’in sa-kai ya samu raunuka a harin, kuma yana karɓar jinya a asibitin Murtala Muhammad da ke cikin birnin Kano.
“Rundunar ta fara bincike kan lamarin, kuma ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin amsa tambayoyi,” in ji sanarwar da DSP Abdullahi Kiyawa ya fitar.
A baya-bayan nan, rundunar ‘yan sanda ta jihar ta sanar da haramta gudanar da hawan sallah, yayin da rikicin sarauta tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ke ci gaba da daukar hankalin jama’a.