‘Yan Sanda Sun Haramta Hawan Sallah a Kano Saboda Tsaro
Rundunar ’yan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da hawan Sallah a lokacin bukukuwan ƙaramar Sallah da ke tafe.
Kwamishinan ’yan sanda na Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke birnin Kano.
Ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon bayanan sirri da suka nuna yiwuwar tayar da tarzoma ta hanyar fakewa da hawan Sallah.
“Wannan mataki ya zama dole bayan tattaunawa da hukumomin da suka dace, domin bayanan sirri sun nuna cewa wasu da aka ɗauka haya da masu gidansu na shirin amfani da hawan Sallah wajen haddasa rikici,” in ji kwamishinan.
Sai dai haramcin da rundunar ta sanar ya saba da matsayar Gwamnatin Kano, wacce ta bayyana aniyarta na gudanar da hawan Sallah. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci dukkan masarautun Kano huɗu ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da su shirya gudanar da hawan.
Haka kuma, Sarkin Kano ya rubuta wa hukumomin tsaro wasika yana mai tabbatar da shirinsa na gudanar da wannan bikin al’ada da aka saba yi duk shekara.
Matakin ’yan sanda na ci gaba da tayar da cece-kuce a tsakanin al’ummar jihar, yayin da ake jiran ganin matakin da hukumomin jihar za su dauka kan lamarin.




