June 14, 2025

‘Yan Sanda a Bauchi Sun Kama Ɓarayin Mashin Guda 3

image_editor_output_image-812418067-1734678082838.webp

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama mutum uku da ake zargi da satar wani babur a kauyen Tenti Babba, Jihar Filato.

A cewar sanarwa da Kakakin Rundunar, SP Ahmed Wakil, ya fitar, an kai rahoton satar babur din ne a ranar 16 ga Disamba, 2024, daga wani mutum mai suna Haruna Maguwa, wanda ya bayyana cewa an sace babur dinsa nau’in Boxer daga gidansa.

“An kai rahoton satar babur nau’in Boxer daga gidan Haruna Maguwa a kauyen Tenti Babba da ke karamar hukumar Bokkos, Jihar Filato, a ranar 16 ga Disamba, 2024,” inji Wakil.

Bisa bayanan sirri, jami’an ‘yan sanda daga Cibiyar Runduna ta Toro sun gano wadanda ake zargi, wadanda suka hada da Yakubu Aminu, Abdul Lawal, da Buhari Abdullahi, duk mazauna garin Magama Gumau.

“‘Yan sanda sun karbo babur din da aka sace kuma sun kama wadanda ake zargin,” inji Wakil.

Lokacin bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifin, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.