June 14, 2025

‘Yan Sanda a Bauchi Sun Fara Bincike Kan Mutumin Da Ake Zargi Da Kashe Matarsa

FB_IMG_1740898037003.jpg

Daga The Citizen Reports

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta fara bincike kan zargin kisan kai da aka yi a ranar 1 ga Maris, 2025, da misalin karfe 11:30 na dare a kusa da Government Girls College, unguwar Fadamam Mada, Bauchi.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Lahadi, lamarin ya faro ne daga saɓani tsakanin wani ɗan kasuwa a Central Market Bauchi, Alhaji Nuru Isah, mai shekaru 50, da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi, mai shekaru 24.

Rahotanni sun nuna cewa sabanin ya samo asali ne kan yadda za a sarrafa kayan abinci da ‘ya’yan itatuwa da aka tanada don bude baki a watan Ramadan, wanda daga nan ya rikide zuwa tashin hankali.

Binciken farko ya nuna cewa Alhaji Nuru Isah ya bugi matarsa da bulala, lamarin da ya sa ta fadi ba ta motsi a cikin gidansu.

An garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na ATBU, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.

‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi tare da kwato bulalar da aka ce ya yi amfani da ita wajen dukan matar. An ajiye gawarta a dakin ajiyar gawa domin gudanar da gwaji.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Auwal Musa Muhammad, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta tabbatar da ganin an yi adalci a wannan lamari.

Haka kuma, ‘yan sanda sun jaddada illar tashin hankalin cikin gida, inda suka bukaci jama’a da su kasance masu mutunta juna, tausayi da fahimta a tsakanin al’umma.

Rundunar ta kuma tabbatar da kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.