Yajin aiki ya sa an rufe ƙofofin zauren majalisun Najeriya
Daga Sabiu Abdullahi
Ginin majalisu a Najeriya da ke Abuja suna rufe yayin ƙungiyoyin ƙwadago suka shiga yajin aiki
Idan dai za a iya tunawa, kungiyar Kwadago ta Najeriya da kungiyar ‘yan kasuwa sun sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin kasar daga yau Talata duk da umarnin da kotu ta bayar na hana kungiyoyin yin hakan.
Rahotannin sun nuna cewa a makon da ya gabata kungiyar ƙwadagon ta fitar da sanarwar yajin aikin a faɗin kasar sakamakon wani hari da aka kai wa Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC, a ranar 1 ga Nuwamba, 2023, a jihar Imo.
Da misalin karfe 12:23 na daren ranar Talata lokacin da ƴan jarida suka ziyarci harabar majalisar, dukkanin kofofin da kai ga zuwa harabar majalisar na kulle da makulli.
An ga ma’aikata da dama sun maƙale a ƙofar shiga majalisar, sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa, duk da kulle-kullen da aka yi, zaman majalisar na ci gaba da gudana a zauren majalisar har ya zuwa lokacin da wannan rahoto ya fito.