Yahudawa masu zafin ra’ayi sun yi ƙoƙarin hana ɗan jarida ɗaukar rahoto a Tel Aviv
Daga Sabiu Abdullahi
Masu tsatsauran ra’ayin ƙasar Yahudawa ta Isra’ila sun yi ƙoƙarin hana wani ɗan jarida daga ɗaukar rahoto game da zanga-zangar da ake gudanarwa dangane da ƙin jinin gwamnatin Isra’ila da buƙatar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.
TRT Hausa ta ruwaito cewa ɗan jaridar wakili ne na kafar watsa labarai ta TRT sashen Larabci a birnin Tel Aviv da ke Isra’ila.
Rahoton TRT ya ce, ‘Masu zanga-zanga ƴan Isra’la da kuma iyalan waɗanda ake riƙe da su a Gaza sun rufe babbar hanyar Tel Aviv a ranar Asabar inda suke ta zanga-zanga dangane da gwamnatin Firaiminista Benjamin Netanyahu mai tsatsauran ra’ayi dangane da watsi da bukatar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni a Gaza.
‘Bayan harin da Yahudawa masu tsatsauran ra’ayi suka kai wanda ya kawo cikas ga ɗaukar rahoton, wakilin TRT na sashen Larabci Fehmi Shtewe ya wallafa labari a shafinsa na X inda yake cewa, “Har wa yau, ƴan Isra’ila sun ƙara kai mana hari, a wannan karon daga tsakiyar Tel viv, inda suka yi yunƙurin hana mu kawo rahoto dangane da zanga-zangar da fusatattun ƴan Isra’ila ke yi dangane da yaƙin Gaza da kuma gaza samun nasarar a yaƙi bayan kwanaki 127! Za mu ci gaba da kawo rahoto na gaskiya!”
‘Ba wannan ne karo na farko ba da masu tsatsauran ra’ayin Isra’ila ko sojojin Isra’ila suke kai hari kan wakilan sashen Larabci na TRT ba.
‘Ko a watan Oktoban da ya gabata sai da sojojin na Isra’ila suka kai hari ga ƴan jaridar TRT kan iyakar Lebanon da Isra’ila a lokacin da suke ƙoƙarin kawo rahoto dangane da rikicin Hamas da Isra’ila.’