April 26, 2025

Yahaya Bello ya cire $720,000 daga asusun Kogi don biyan kuɗin makarantar yara—Shugaban EFCC

images-2-28.jpeg

By Sabiu Abdullahi

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya tura dala 720,000 daga asusun gwamnati zuwa wani ofishin canji kafin ya bar ofis domin biyan kudin makarantar yaronsa.

Olukoyede ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata a Abuja.

Ya ce, “Wani gwamna mai ci da yake ya san zai tafi ne kai tsaye ya dauko kudi daga gwamnati zuwa ofis, ya yi amfani da su wajen biyan kudin makarantar yara, dala 720,000, da tsammanin zai bar gwamnati. 

“A jihar da ke fama da talauci kamar Kogi, kuma kuna so in rufe idona a kan hakan da sunan ‘Ana amfani da ni’. Wa zai yi amfani da ni a wannan matakin rayuwar tawa?”

Olukoyede ya ci gaba da cewa shi da kan sa ya tuntubi Bello, inda ya ba shi dama ya fayyace lamarin a cikin wani yanayi na girmamawa a ofishin EFCC amma tsohon gwamnan ya ki bayar da hadin kai.

14 thoughts on “Yahaya Bello ya cire $720,000 daga asusun Kogi don biyan kuɗin makarantar yara—Shugaban EFCC

Comments are closed.