Yadda Emefiele ya yi buga jabun takardu har ya sace $ miliyan 6 daga asusun gwamnatin—Boss Mustapha
Daga Sabiu Abdullahi
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya bayyana a ranar Talata cewa an fitar da dala miliyan 6.2 daga babban bankin Najeriya a watan Fabrairun 2023 ta hanyar amfani da takardun jabu.
Ya ce an fitar da kuɗin ne ga masu sa-ido na ƙasashen waje gabanin babban zaben shekarar 2023.
Mustapha ya faɗi haka ne a lokacin da ya bayyana a matsayin mai shaida na huɗu a ci gaba da shari’ar damfara da ake yi wa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, a gaban babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama, Abuja.
Hukumar EFCC dai ta gurfanar da Emefiele a gaban kuliya a kan laifuka 20, da suka hada da jabun takardu, da hada baki, da cin gajiya a haramce, da kuma cin amana da sauransu.
Musamman, EFCC ta zargi Emefiele da yin bayyana kansa a matsayin sakataren gwamnati don samun kuɗi $6.2m daga babbybankin ba bisa ka’ida ba.
EFCC ta yi zargin cewa a ranar 8 ga Fabrairu, 2023, Emefiele ya haɗa baki da Odoh Ocheme don samun dala miliyan 6.2 daga bankin CBN.
A cewar EFCC, Emefiele ya yi ikirarin cewa SGF ya buƙaci CBN da ta saki dala miliyan 6,230,000.00 saboda umarnin shugaban kasa ne.