January 15, 2025

Yadda ambaliyar da aka yi a Borno ta yi kaca-kaca wa ƴanta’addan BH

0
IMG-20240910-WA0014

Daga Sabiu Abdullahi  

Wata mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa dajin Sambisa da ke jihar Borno, inda ta kashe mayakan Boko Haram da dama da suka hada da mata da ƙananan yaran cikinsu.  

Rahotanni sun kuma ce ambaliya ta lalata matsugunin ƴanta’addan a yankin Dollarland. 

Wani shahararren ɗanjarida a Najeriya, Jaafar Jaafar, ya ce, “Allah Ka afka wa sheɗanun Sambisa da na dazukan Zamfara da Sokoto da Katsina da Kaduna da Niger mummunar ambaliyar ruwa. Ruwa, tafi da su, kar ka dawo su!”

Majiya mai tushe daga cikin jami’an tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda wani rahoton Daily Trust ya nuna.   

A cewar wata majiya kuma, ambaliyar ta afku ne da misalin karfe biyu na safe lokacin da akasarin maharan ke barci.  

Ambaliyar ta kuma ɗaiɗaita mahara da dama a yankin Gwoza tare da lalata wani bangare na tsohon gidan yari, inda aka kwashe fursunoni da dama zuwa sabon gidan yari mai tsaro a Maiduguri.  

Sannan wata majiyar tsaro kuma ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safe.   

An kuma samu labarin an kwashe wasu fursunonin gidan yarin, da akwai yiwuwar za su iya tserewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *