January 15, 2025

Yadda ake shirye-shiryen miƙa wa Sanusi II ragamar mulki

13
IMG-20240524-WA0006.jpg


Daga Abdullahi I. Adam

Shirye-shirye sun kankama don miƙa takardar soma aiki ga  Muhammadu Sanusi II  a Kano.

Rahoton da TCR Hausa ta samu ya nuna cewa a yanzu haka ɗakin taro na Afirka da ke cikin gidan gwamnatin jihar, ya ɗauki harama, inda aka masa maƙil da kujeru da kayayyakin ado domin gudanar da taron.

Tuni ma’aikatan gidan gwamnatin su ka killiƙa sunayen manyan baƙi a kan kujeru don gabatar da taron na yau.

TCR Hausa za ta ci gaba da kawo maku halin da ake ciki idan an soma taron.

13 thoughts on “Yadda ake shirye-shiryen miƙa wa Sanusi II ragamar mulki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *