November 14, 2025

Yadda Abdulmumin Kofa Ya Samu Tarba A Majalisa Bayan Ya Koma APC

0
FB_IMG_1763061396304-1024x683

Daga TCR Hausa

Dan majalisar wakilai na Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sake komawa jam’iyyar APC tare da Rt. Hon. Sagir Koki na Kano Municipal.

A rubutunsa da ya yi a Facebook, Kofa ya ce: “A yau na shiga jam’iyyar APC a hukumance tare da ɗan’uwana, Rt. Hon. Sagir Koki, dan majalisar da ke wakiltar Kano Municipal da kewaye.”

Ya ce an tarbe su da karamci a Majalisar Wakilai daga manyan jami’an siyasa, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; manyan jami’an majalisa; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila; Shugaban APC na kasa, Prof. Nentawe Yilwatda; da tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Kofa ya ƙara da cewa: “Ina miƙa godiya ta musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, GCON, da sauran manyan jami’ai, ’yan majalisa da sanatoci bisa tarbar kirki.”

Ya ce za su ci gaba da aiki tare domin hidimar kasar nan cikin jajircewa da sadaukarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *