Yadda ƙasashen Yamma ke ɗaukar lamarin Isra’ila da zafi
Daga Muhsin Ibrahim
Ɗaya daga cikin abubuwan mamakin da na gani zuwa na Amerika shekerar da ta gabata shi ne huɗubar limamin masallacin jumu’ar na muka yi sallah. Balarabe ne.
Ya caccaki Amerika da sauran ƙasashen da suke goya wa Isra’ila baya sosai. Sai da yai maganar kuɗin da Amerika ke ba wa Isra’ila bayan suna da marasa gida (homeless),dss. a garin da na je (San Francisco).
Yau wasu “activists” suka saka wata fasta a gaban masallacinmu a nan Cologne, Germany, da take kira da a ƙauracewa dabinon Isra’ila. Zo ka ga yadda shugabannin masallacin suka hasala. Ɗaya daga cikinsu ya yage ta, yai ta faɗa kuma. Suma Larabawa ne, yawanci daga Morocco.
Gaskiya an saka wa mutane fargaba da tsoro kan duk wata magana da ta danganci Isra’ila a nan sama da ko’ina. Kowa yana tsoron a zarge shi da tsanar Yahudawa (antisemitism), wanda zai iya jawo wa mutum hukunci mai tsanani.
Ɗazu na karanta cewar daga yanzu sai ka yadda da zaman Isra’ila ƙasa ka kuma amsa wasu tambayoyi har 12 a jarabawar zama ɗan ƙasa a Germany. Kai, har Bayahude ɗan Isra’ila an zarga da “antisemitism” a ƙasar nan! Duniya.
A Amerika ma ana hukunta mutane kan faɗar ra’ayinsu kan Isra’ila, amma bai kai Germany da wasu ƙasashen yamma ba. Shi ya sa wancan limamin ya iya waccan huɗubar.
Allah ya kawo ƙasashen yaƙin nan na Gaza da ma sauran wajaje irin Zamfara, Katsina, Sudan, amin. Allah kuma ya tsare mu, amin.
Muhsin Ibrahim malamin harshen Hausa ne a Jami’ar Cologne da ke kasar Jamus.