January 14, 2025

Ya kamata kowa ya nemi makami domin kare kansa a Arewa—Sheikh Bello Yabo

48
images (9) (12)

Daga Sabiu Abdullahi  

Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Najeriya, Muhammad Bello Aliyu Yabo, ya yi kira ga ‘yan kasar da su dauki matakin kare kansu da iyalansu, sakamakon karuwar barazanar ta’addanci a Arewacin Najeriya.  

Da yake jawabi ga wata jama’ar yankin Arewa, Yabo ya bayyana muhimmancin kare kai, ya kuma bukaci ‘yan kasar da su mallaki makamai domin kare kansu daga karuwar ayyukan ta’addanci.    

Da yake mayar da martani game da kisan da aka yi wa Sarkin Gobir na gundumar Gatawa a Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Muhammad Bawa, Yabo ya ce, “Yaya za ku iya tsayawa ku kalli wani mai laifi ya shigo gidanku, ya sace matar ku, ko ya yi garkuwa da ku alhali yana amfani da makaminsa?”  

Kalaman malamin na zuwa ne bayan kisan gillar da aka yi wa Bawa, wanda masu garkuwa da mutane suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 60 da babura biyar domin a sako gawarsa domin a binne shi yadda ya kamata.  

48 thoughts on “Ya kamata kowa ya nemi makami domin kare kansa a Arewa—Sheikh Bello Yabo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *