Ya kamata jimi’o’i sai sun fara ba wa duka ɗalibai mata ɗakunan kwana kafin su fara ba wa maza—Dr. Tilde
Daga Sabiu Abdullahi
Tsohon Kwamishina Ilimi na Jihar Bauchi Dr. Aliyu Usman Tilde ya yi kira ga hukumomi da su sauƙaƙa wa ɗalibai mata a jami’o’i ta hanyar fara ba su ɗakunan kwana kafin su bayar wa maza.
A cewarsa, sai bayan duka mata sun gama samun ɗakina cikin jami’a kafin a ba wa maza saboda ƙin yin hakan fitina ce.
Ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.
Ya ce: “Ya kamata manyan makarantu su ba da duk dakunan kwanansu ga dalibai mata kafin in sun rage su ba wa maza. Kama dakuna ga yanmata a waje fitina ce.”
Ya ƙara da cewa, “A nan ina jinjina wa ABU Zaria. Tun 1986 da MSS ta ba da shawarar a kara wa mata hostels maimakon off campus hukumar jami’an ke kara hostels na mata, yau har ya hada da Ribadu, da Alex da Suleiman hall.
“A gaskiya mu iyaye Allah kadai ya san bakin cikin da muke ciki a kan rashin hostels ga yayanmu mata. Abu ne kuma mai saukin warwarewa amma ba a damu ba.
“Haka nan ya kamata hukuma ta yawaita hostels din. Wasu makarantun an yi shekaru kusan 50 ba a kara ko daki daya ba, misali ABU ba dan Dangote ya ba da gudummawa ba a yan shekarun nan. Amma admissions sai a yi ta yi ba a damu da facilities da welfare na dalibai ba, VC after VC, nan kuwa ga gine gine manya manya kullum ana yi har da wadanda ba a bukata.”
Wannan magana ba za ta rasa nasaba da zarge-zargen aikata baɗala ake zargin ana yi a gidajen ɗalibai mata wanda ba a cikin harabar jami’a yake ba.
Tun bayan samamen da hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kai wasu wurare a jihar ake ta muhawara game da kasancewar ɗaliban a wajen jami’a.