Ya kamata a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa—Firaiministan Chadi
Daga Sodiqat Aisha Umar
Firaiministan Chadi Succes Masra ya shigar da ƙara a majalisar tsarin mulkin ƙasar inda yake ƙalubalantar sakamakon farko na zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ƙasar a makon da ya gabata.
An ayyana Janar Mahamat Deby a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da kashi 61 cikin 100 na ƙuri’un da aka jefa amma Mista Masra na iƙirarin shi ne ya lashe zaɓen.
Ɗan hamayyar da jam’iyyarsa ta Transformer sun nemi a soke sakamakon inda ta yi zargin an yi cushe a akwatunan zaɓen sannan sojoji sun ɗauke wasu domin ƙirga ƙuri’u a wasu wuraren.
An kama wasu ƴan ɓangaren hamayya yayin da Mista Masra da magoyta bayansa ake masu barazana, in ji jam’iyyar.
Sai dai Mista Masra ya nanata cewa magoya bayansa mutane ne masu son zaman lafiya yana mai cewa sauyin da kuke son gani, ba zai faru ba a ƙasar da ta lalace.
Jim kaɗan kafin bayyana sakamakon zaɓen, Mista Masra ya yi kira ga magoya bayansa da su gudanar da zanga-zanga domin kare ƙuri’unsu.