Y America: ‘Yadda Aka Lakaɗa Min Duka Bayan Na Yi Dare A Gidan Kallon Ƙwallo’

Daga MA Iliasu
Da na kalli bidiyon ɗan Tiktok ɗin da ƴan uwansa suka zane, sai na tuna da shekarar 2007 lokacin da naje kallon El-Classico nayi dare. A lokacin ƙarfe tara ake rufe ƙofar gidanmu. Sai aka samu akasi a daidai lokacinne ma za’a take wasa. Ai kuwa nayi saɗaf na fice na tafi gidan kallon ƙwallo. Kafin na dawo 11:45 tayi. Ina dawowa na banƙare rodin tagar waje na shiga cikin shagon ƙofar gida, na salallaɓa na shiga cikin gidan. Dana shiga sai naji tsit, alamar kowa yayi bacci, don haka sai hankalina ya kwanta, na shiga cikin parlour ina laluben ƙofar ɗakinmu.
Ai kuwa kwatsam sai naji na taɓa gemu! Sai gabana ya yanke ya faɗi. Ashe ƙofar rago suka yi min. Tun ƙarfe goma ake nemana lungu da saƙo har aka gaji aka dawo gida. Gaba ɗaya ƴan gidan sun tsaya cirko-cirko suna jiran suga ta ina zan ɓullo. Yayyena daga me bulala sai me wayar rediyo. Wasu ma don ƙeta har da ɗaukar maburgi da muciya. Gashi gida gidan yawa. Kuma megida ne ya bayar da odar cewa a bani kashi!
Habawa! Ai ana kunna ƙwan fitilar parlour sai suka yo kaina da bugu. Ji kake tsut! tsut!! tsut!!! Bulalai nata sauka a jikina. Wannan yace ‘don ubanka in kaje?’ ‘wancan yace don ubanka sai mun karyaka muga ƙafar yawo!’ Wasu ma bana jin me suke cewa.
Shi kuma babanmu yayi tsaye akan ‘balconey’ yana ce musu ‘ku bashi kashi, bai daku ba, kar ku sake shi sai yayi laushi!’ Su kuma mugayen kamar an watsawa wuta fetur. Dama akwai masu jin haushina, sai suka samu ikon tumurmusani kamar tuwon gidan suna!
Can maƙwabta suka ji ihun ya yi yawa sai Hajiya Me Tuwo (Allah ya jiƙanta) ta shigo tace jama’a me yake faruwa ne? Laifin me ya yi? Sai babanmu ya ce ai ba’a zo wurin jin bahasi ba, sai ya yi laushi tukunna zamu ji ina yaje. Sai ta roƙi arziƙi a sake ni haka a tambayi ina na tafi. Sai babarmu, wadda tafi kowa zaƙewa wurin buguna, tace ‘ina kaje?’ Nace ai el-classico naje kallo!
Sai takaici ya kama babanmu ya yi min gatse yace, ‘to suwa aka ci?’ Ni kuma sokon ban gane ba sai nace ai ni babu zakarana a wasan, ni ɗan Arsenal ne! Yace ‘toh madallah kuci ubansa!’ Ni dai da ƙyar Me Tuwo ta ƙwace ni a hannun mutanen gida!
Shi yasa kwanaki wani ja’irin yaro yazo wai dani zai yi musun ƙwallon ƙafa, har ma yake cewa wai ai mu Arsenal babu abinda muka taɓa ci don haka ya fi ni sanin ƙwallo. Kawai na yi shiru na tashi na tafi. Don idan na tsaya tas zan kwafɗe shi! 😣
Yeni kullanıcı hediye bonusu 🉠🌟 Yüksek Kazançlar İçin Hızla FreeSpin ile Slot Oyunlarına Başla! https://kusadasi.kalp-escort.com/
özgürlüğün seni bekliyor 🀠💠FreeSpin Şansınla Büyük Paralar Kazan, Eğlenceden Kopma! https://kusadasi-bayans9.escortlariniz.com/