Xavi Ya Sanar Da Aniyarsa Ta Barin Barcelona A Ƙarshen Kakar Wasan Bana
Daga Sabiu Abdullahi
Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar a watan Yuni, wanda ya kawo karshen kakar wasa mai cike da kalubale.
Matakin ya biyo bayan gagarumin koma baya ne a lokacin da Barcelona ta sha kashi da ci 5-3 a hannun Villareal mai matsayi na 14 a teburin Laliga a daren Asabar.
Dan jaridar wasanni Fabrizio Romano ne ya bayyana hakan, inda ya ambato Xavi, wanda ya bayyana cewa, “Mun kai matsayin da ba za a sake dawowa ba, lokaci ya yi da za a yi sauyi, ina ganin lokaci ya yi da zan tafi, na yi magana da jagororin kungiyar zan tafi ranar 30 ga watan Yuni.”
Xavi, wanda ya yi fice a tarihin Barcelona, ya shafe shekaru 17 a matsayin dan wasa, inda ya ba da gudummawa a wasanni 767, ya kuma lashe kofuna 25, ciki har da kofunan lig guda takwas da na gasar zakarun Turai hudu.