January 15, 2025

X (Twitter) ya rufe ofishinsa na Brazil

0
images (8) (14)

Daga Sabiu Abdullahi  

X, dandalin sada zumunta mallakin Elon Musk, ya rufe ofishinsa na Brazil, a matsayin martani ga takaddama da alkalin kotun kolin Alexandre de Moraes, kan bukatar tantancewa abubuwan DA’AKE wallafawa a dandalin.

Dandalin ya ki bin umarnin alkali na toshe akawun da ake zargi da yada labaran karya, wanda ya kai ga barazanar kamawa da kuma tara.  

A cikin wata sanarwa, X ya nuna cewa ma’aikatansa na Brazil ba su da ikon hana daura ko toshe wani abu da aka ɗora a dandalin, amma duk da haka alkali de Moraes ya yi musu barazana.  

Kamfanin ya ce, “Don kare lafiyar ma’aikatanmu, mun yanke shawarar rufe ayyukanmu a Brazil. Alhakin ya rataya ne kawai ga Alexandre de Moraes. Ayyukansa sun sabawa gwamnatin dimokuradiyya.”  

Musk, mamallakin X ya soki alƙali de Moraes a bainar jama’a, yana mai cewa. 

Duk da rufe ofishin, masu amfani da shafin a Brazil har yanzu suna iya ci gaba da amfani da shi.

Har yanzu dai kotun kolin Brazil ba ta ce uffan ba kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *