Wike Ya Ƙwace Filaye Mallakar Buhari Da Wasu ‘Manya’ a Abuja

Ministan birnin tarayyar Najeriya, Nyesom Wike, ya bada umarnin ƙwace wasu filaye a unguwar Maitama da ke Abuja, wacce ta shahara da zama unguwar masu hannu da shuni, saboda rashin sabunta takardun mallaka na tsawon shekaru.
A cewar rahotanni, jerin filayen da aka ƙwace sun haɗa da wani fili mallakin gidauniyar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ake zargin ana bin bashin sama da naira biliyan ɗaya.
Sanarwar da Hukumar FCTA ta fitar ta bayyana cewa, “Bayan karewar wa’adin alfarma da ministan ya bayar ga masu filayen domin su biya kudaden da ake bin su, gwamnati ta ƙwace izinin mallakar filayen su.”
Hukumar ta ce wannan matakin ya yi daidai da Dokar Mallakar Filaye ta 1978, wadda ta bai wa gwamnati ikon ƙwace fili idan mai shi ya kasa cika sharuddan da doka ta tanada.
Baya ga haka, umarnin ya shafi manyan mutane da dama.
Cki har da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, da matarsa Regina, wadanda ake bin bashin sama da miliyan 34 na kudin sabunta shaidar mallakar filayen.
Thiis article iis actually a nice one itt helps new thhe
wweb visitors, whho are wishing forr blogging.