December 7, 2025

Wata miyar sai a maƙwabta: Gwamnatin Chadi za ta samar da ruwa da wuta kyauta ga ƴan ƙasa

images-245.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin kasar Chadi ta sanar da cewa za ta samar da ruwan sha da wutar lantarki kyauta ga gidaje har zuwa karshen shekara.

Yawan amfanin gida na wata-wata da gwamnati ke biya ya kayyade kan mita 15 (lita 15,000) na ruwa da wutar lantarki 300 kWh.

Gwamnati a ranar Litinin ta ce za ta kuma yafe kudaden ruwa da wutar lantarki ga mazauna da ke da basussuka.

Har ila yau, ta sanar da rage harajin safarar kayayyaki da ka iya rage farashin sufuri, wanda ya haura a watan da ya gabata tare da karin farashin man fetur.

wata sanarwar hadin gwiwa da fadar shugaban kasar da ministan kudi suka fitar ta ce Shugaban mulkin sojan Chadi kuma shugaban rikon kwarya Mahamat Déby ya amince da manufar “taimakawa gidaje.”

Wasu mazauna yankin kuma sun ce matakin ba shi da ma’ana saboda wasu sassa a N’Djamena babban birnin kasar sun fuskanci katsewar wutar lantarki tsawon makonni biyu da suka gabata.

Sai dai wasu ‘yan kasar ta Chadi sun yi na’am da matakin a matsayin agajin da ake bukata ga matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita.