Wata cutar ciwon ciki da zawayi ta kama sojojin Isra’ila da ke yaƙi a Falasɗinu
Daga Sabiu Abdullahi
Kafofin yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa sojojin Isra’ila da aka girke a zirin Gaza suna fama da barkewar cututtuka na ciwon ciki da gubar abinci.
Yedioth Ahronoth ya ruwaito a ranar Litinin cewa “An sami karuwar cututtukan hanji a tsakanin sojojin na Isra’ila.”
Rahoton ya ce tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-hare a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, yawancin gidajen cin abinci da daidaikun jama’a sun ba da gudummawar kayayyakin abinci ga sojojin Isra’ila, wadanda watakila suka gurbace a lokacin shirye-shirye, sufuri ko kuma ajiya, in ji rahoton.
Sojoji da dama sun fuskanci alamun shan guba a abinci, wanda ya hada da zawo mai tsanani da kuma yanayin zafi.
Tal Brosh, darektan sashin kula da cututtuka a babban asibitin Assuta da ke Ashdod ya ce, cutar zawo ta yadu a tsakanin sojojin da ke kudancin kasar, a wuraren taro, daga baya kuma a cikin sojojin da suka je yaki a cikin Gaza.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da faɗa tsakanin Isra’ila da Falasdinawa ke kara ta’azzara.