Wata cibiya a Saudiyya ta ɗauki nauyin raba wasu tagwayen da suka manne a Kano
![IMG_3224.jpeg](https://tcrhausa.com/wp-content/uploads/2023/10/IMG_3224.jpeg)
Daga Sabiu Abdullahi
Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman (KSARelief) da ke kasar Saudiyya ta bayyana shirin gudanar da aikin tiyatar raba wasu tagwaye Hassana da Husaina Hassan Isa daga Kano, Najeriya.
Muhammad Alsahabi, mai magana da yawun ofishin jakadancin Saudiyya a Abuja ne ya sanar da hakan.
Hassana da Husaina, wadanda suka haɗe a kirji da kuma wasu muhimman gaɓoɓin jiki, suna fuskantar wasy matakan masu sarƙaƙiya a wajen raba su.
Labarin nasu ya ɗauki hankalin miliyoyin mutane a duk duniya.
Yana kuma nuna buƙatar gaggawa don samun kulawar likita ta musamman ga irin waɗannan matsalolin.