January 24, 2025

Wata amarya ta hallaka mijinta har lahira a Neja

14
image_editor_output_image143516336-1707756518927.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Wani abin takaici ya faru a kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Lapai a jihar Neja, yayin da wata sabuwar aure mai suna Aisha Aliyu ‘yar shekara 20 ta kashe mijinta mai suna Idris Ahmadu.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 1 na safiyar ranar Litinin, ya jefa al’ummar cikin firgici da rashin aminci.

Rahotanni da suka fito daga mazauna garin sun bayyana cewa, ma’auratan an ɗaura aurensu ne a ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa sun samu wata ‘yar karamar takaddama ne wacce ta taso a tsakaninsu a yammacin Lahadi, wanda da alama sun sasanta kafin su kwanta.

Sai da tsakar dare mahaifiyar marigayin ta samu lamarin al’amarin bayan faruwarsa.

Da suka garzaya wurin tare da wasu mazauna garin, sai suka gamu da Idris Ahmadu kwance a cikin tafkin jini.

Da alama a lokacin ymyana ƙoƙarin guduwa ne amma sai dai ya yi halinsa a daidai bakin ƙofar.

Shaidun gani-da-ido sun bayyana cewa Aisha ta daɓa wa mijin nata wuƙa ne a ƙirji kafin ta yi masa yankan rago.

Wasu majiyoyi na kusa da ma’auratan kuma sun bayyana cewa a yayin da suka shafe shekaru suna soyayya da junansu, Aisha ta bayyana buƙatar auren wani daban kafin daga bisani ta amince ta auri Idris.

Duk da haka, ya bayyana cewa rikice-rikice tsakaninsu sun ci gaba da faruwa, wanda ya haifar da wannan mummunan sakamakon.

14 thoughts on “Wata amarya ta hallaka mijinta har lahira a Neja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *